Haaland ya ci uku rigis karo na hudu a Premier a Etihad a bana

23 Jan 2023

Erling Haaland

Asalin hoton, Getty Images

22 Janairu 2023

Manchester City ta doke Wolverhampton da ci 3-0 a wasan makon na 21 a gasar Premier League da suka kara ranar Lahadi a Etihad.

Erling Haaland ne ya ci dukkan kwallayen a wasa, wanda ya fara cin ta farko saura minti biyar a yi hutu.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne dan wasan ya kara na biyu a bugun fenariti, sannan ya zura na uku a raga a minti na 54, minti hudu tsakani da na biyu.

Karo na hudu kenan da Haaland ya zura uku a raga a gasar Premier League a kakar nan.

Ya kara da cin Crystal Palace a karawar Premier da City ta yi nasara da ci 4-2 ranar 27 ga watan Agustan 2022.

Makon gaba Haaland ya kara cin kwallo uku rigis a karawar da City ta yi nasara a kan Nottingham Forest da ci 6-0 a daii Premier League.

A wasan hamayya na 'yan birbin Landan Haaland ya kara zura uku rigis a ragar Manchester United a wasan da Manchester City ta ci 6-3.

Jerin wasannin da Haaland ya ci kwallo uku rigis a Premier League a bana

Premier League Asabar 27 ga watan Agustan 2022       

Man City    4 - 2  Crystal Palace    

Premier League Laraba 31 ga watan Agustan 2022     

Man City    6 - 0  Nottm Forest    

Premier League Lahadi 2 ga watan Oktoban 2022       

Man City    6 - 3  Man Utd   

Premier League Lahadi 22 ga watan Janairun 2023

Read more
Similar news