'Ba mu so azumi ya wuce ba saboda za mu daina cin shinkafa'

16 days ago

Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock

Sa'o'i 2 da suka wuce

Mu - Figure 1
Photo BBC News

A ranar Talata ne, musulmi a faɗin duniya suka kammala azumin watan Ramadan da a cikinsa ake rabauta da ɗumbin lada na ayyukan ibada.

A watan mutane da dama su kan rungumi ɗabi'ar ciyar da marasa galihu da masu tsananin buƙatar taimako saboda ciyarwa a cikin watan na da gwaggwaɓan lada.

Sai dai wucewar watan ya sa mabuƙata cikin zulumi da fargaba na tunanin yadda rayuwa za ta ci gaba kasancewar rashin samun abincin tallafin da wasu ke yi don raba wa mabuƙata.

Irin wannan ce fargabar da wata uwa Aisha Yusha'u a jihar Kano ta shiga kasancewar mijinta ya rasu a baya-bayan nan ga kuma yara shida marayu da ke gabanta ƴan shekara tsakanin uku zuwa 15.

A hirar da BBC ta yi da Aisha wadda take takaba a lokacin hirar, ta ce ƴaƴanta a kullum suna tambayar ta: "Umma, yanzu ba za a samu kunu ba, yanzu an daina cin shinkafa?".

Mahaifiyar ta ce ita da yaranta sun cinye ɗan jarin da take juyawa wajen yin cefanen kayan buɗa baki a lokacin azumi.

"Gaskiya jarin nan mun cinye shi , yanzu kam babu shi, ba mu da wata mafita sai yadda Allah ya yi da mu." in ji ta.

Aisha ta yi waiwaye kan ranar da aka tashi da azumi inda ta ce na farko sun yi ɗore ne saboda rashin abincin da za su ci.

"Muka kai azumin nan a ɗore, muka sha ruwa ba mu da komai, ba mu yi sahur ba, ba ni da shi a ranar." in ji ta.

Ban ƙi a ci gaba da azumi ba...

Aisha Yusha'u ta shaida wa BBC cewa rayuwar babu da suke ciki bayan tafiyar watan Ramadan ya sa tana jin gwara a ci gaba da azumi kawai tun da a watan Ramadan suna samun tallafin abinci.

"A yi ta azumi, ana samun ladan ibada, ga mutane suna ta samun ladan marayunmu, idan can an ba ka, wancan ya ƙara maka." kamar yadda ta bayyana.

Ta ce a duk ranar da suka wayi gari babu abincin da za su saka a bakin salati, to tana komawa gefe ta yi ta zubar da hawaye inda yaran nata ba za su ga halin da take ciki ba.

"Babu mai yi min kuka a cikinsu sai dai ka gan su sun yi abin tausayi, ni ce dai mai yin kuka, idan sun yi lamo sun jeru." kamar yadda ta bayyana.

Ba mu da mafita sai yadda Allah ya yi...

Mahaifiyar ta bayyana cewa muna ta faɗa wa Allah ya kawo mana mafita, ba mu da wata hanyar kamawa sai yadda Allah ya yi da mu."

Ta bayyana yadda take ƙoƙarin ciyar da yaranta kafin azumi inda ta ce idan suka yi sana'a, suna samun abin da za su ci duk da cewa ba wai yana isar su ba ne.

"Idan mun yi sana'a za mu raba ɗan kunun da muka yi za mu ɗibi roba ko biyu ne mu rarraba, na ɗeba musu ƙosai na hamsin-hamsin,"

"Idan rana ta yi, aka yi abincin siyarwa aka gama, shi ma zan ɗiba haka dai sai na karkasa, kowa sai ya ɗiba ya ci." in ji ta.

Daga nan kuma kamar yadda ta shaida mani sai ta nemi yaran su je su yi ta addu'a Allah ya bayar da yadda za a yi su samu abincin da za su ci da dare.

"Muna fatan masu hali su ci gaba da tallafa wa mabuƙata". In ji Aisha.

A cewar Aisha, uwar marayu, rashin samun taimako musamman ga irinsu mabukata yana iya kawo masu cikas wajen tafiyar da harkokinsu na rayuwa kamar sauran jama'a.

"Idan aka ce babu mai taimakon ka duk da kai ba ka da yadda za ka yi, fatanmu Allah ya horewa masu yin su bayar." kamar yadda ta bayyana.

"Akwai mutane da yawa irin mu, idan an taimaka ana samun lada ba kaɗan ba." in ji ta.

Read more
Similar news